25 Agusta 2021 - 10:10
​Iran:Samuwar Sojojin Ruwa Na Kasar Iran A Tekun Atlantika Ya Sanya Damuwa Ga Kasar Amurka

Mataimakin kwamandan sojoji ruwa na kasar Iran ya ce samuwar sojojin Iran a yankuna daban-daban na tekuna a duniya wata matsalace ga kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : ya nakalto Rea Admiral Hamzeh Kaviani yana fadar haka a lokacin bude gasar wasannin ruwa wadanda suka hada da tseren jiragen ruwa na kasashen yankin Asia da takun Caspian a tashar jiragen ruwa na Bandar Anzali dake arewacin kasar Iran.

Kaviani ya kara da cewa a halin yanzu ya tabbata ga kasashen duniya kan cewa Iran tana bada gudumawa mai yawa wajen tabbatar da zaman lafiya a tekun Farisa da wajensa. Sabanin irin farfagandar da Isra’ila da kawayenta suke yadawa.

Kaviani ya kammala da cewa a halin yanzu jiragen yakin Iran suna wucewa ta mashigar ruwa ta Suiz ta shiga tekun Mediteranain, ta je har North Sea. Banda haka tana zuwa dukkan takenan masu muhimmanci a duniya.

342/